Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello

0
49

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan kudi naira miliyan 500.

Kotun ta bayar da belin ne a yayin zaman ta na yau Juma’a wanda mai shari’a Emeka Nwite, ya jagoranta.

kotun ta nemi Yahaya Bello, ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa kafin a sake shi, Kuma dole ne mutanen da za su tsaya masa su kasance sun mallaki kadarori a Abuja.

Tun da farko hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da shi kan zargin almundahanar kudaden jihar Kogi da yawan su yakai naira biliyan 110.

Sai dai Yahaya Bello ya musanta zargin sace kudaden.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here