NAFDAC ta lalata jabun magani da kudin sa zarce naira biliyan 10

0
262

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta samu nasarar lalata jabun magani da wanda lokacin amfani dasu ya kare, da kuma wadanda basu da rijista da hukumar da darajar kudin su ta zarta naira biliyan goma.

:::Mayakan Boko Haram sun yanka masu kamun kifi su 14 a iyakar Najeriaya da Nijar

Shugabar hukumar Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye, ce ta jagoranci kone magungunan a wajen zuba shara na Akinyele dake jihar Ibadan, sannan tace an kama jabun maganin a jihohi 5 na kudu maso maso yammacin Nigeria da kuma jihar Kwara.

Daraktar hukumar NAFDAC shiyyar kudu maso yamma Roseline O. Ajayi, ce ta yi bayani a madadin shugabar hukumar ta kasa.

Hukumar NAFDAC ta nemi hadin kan yan kasa dasu bata hadin kai don samun nasarar magance matsalar siyarwa da mutane jabun magunguna inda hukumar tace suna taka rawa wajen cutar da lafiyar al’umma da saka musu cutuka daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here