Jirgin sama ya sauka daga titin sa bayan tayar sa ta fashe a Abuja

0
103

Wani jirgin daukar kaya ya gamu da fashewar taya lokacin daya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikwe, dake birnin tarayya Abuja, wanda hakan ya zama sanadiyyar kaucewar jirgin daga titin sa zuwa cikin dajin dake cikin filin jirgin, a yau laraba.

:::Gobarar kasuwar Alaba Rago ta haifar da asara a jihar Lagos

Tuni dai hukumar kula da filayen jirgin sama ta kasa ta rufe titin jirgin na dan wani lokaci zuwa komai ya daidaita.

Zuwa yanzu an bayar da rahoton cewa daukacin mutanen dake cikin jirgin su 5 sun tsira da rayuwar su ba tare da jin ciwo ba.

Lamarin ya haifar da tsaiko a yanayin hada-hadar tashi da saukar jiragen sama a filin na Nnamdi Azikwe, yayin da ake kokarin gyara wurin daya samu matsala daga titin jirgin.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar FAAN mai kula da filayen tashi da saukar jiragen saman Nigeria Obiageli Orah, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin sanarwar daya fitar a yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here