Yan fashi da makami sun kashe kanwar Gwamnan Jihar Taraba

0
62

Yar uwar gwamnan jihar Taraba mai suna Atsi Kefas, ta gamu da ajalin ta kwanaki 4 bayan wasu yan fashi da makami suka harbe ta lokacin da suke tafiya a Mota tare da mahalifiyar gwamnan a makon daya wuce.

Mamaciyar mai shekaru 44, ta mutu da tsakar daren jiya Litinin a wani asibiti mai zaman kansa dake birnin Tarayya Abuja, inda ake kula da ita bayan ta gamu da iftila’in harbin.

:::Babu wanda zai hana dan arewa neman shugabancin Nigeria—Atiku

Lamarin harbin ya afku a ranar alhamis data gabata lokacin da mahaifiyar Gwamna Agbu Kefas, Jummai Kefas tare da yarta Atsi Kefsa, ke kan hanyar zuwa Wukari, wanda a nan ne yan fashin suka tare motar da suke ciki tare da harbin Atsi.

Kawo lokacin fitar da wannan labari ba’a ji sanarwar mutuwar daga iyalan mamaciyar ba, sai dai jaridar Premium Times, ta rawaito cewa wata sahihiyar majiya ta tabbatar mata da labarin mutuwar tun a daren litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here