Tinubu baya son ganin yan Nigeria a cikin yunwa—Gwamnatin tarayya

0
41

Gwamnatin tarayya ta ce burin shugaban kasar na yanzu shine samar da abinci ga yan kasa don kawar da matsalar yunwa.

Karamin ministan noma na Nigeria Aliyu Abdullahi, yace tun lokacin da aka rantsar da Tinubu a watan Mayun 2023, yake fito da shirye-shirye domin tabbatar da an wadata al’umma da abinci.

Cikin wata hira da gidan talbijin na Sunrise, ya yi da karamin ministan, ya ce a cikin shirye shiryen Tinubu, samar da abinci shi ne kan gaba.

Inda yace hakan zai habbaka tattalin arzikin kasa.

Aliyu Abdullahi, ya ce shugaba Tinubu, ya damu matuka kan matsalar karancin abincin da ake fama da ita, wanda ya ce a wasu lokutan shugaban na sanar da su cewa babban burinsa shi ne ya kai al’ummar Najeriya matsayin da babu wanda zai kwana da yunwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here