Kamfanonin jirgin sama 14 aka tantance don jigilar Maniyyata Hajjin 2025 a Nigeria

0
71

Kamfanonin jiragen sama 14 hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON, ta tantance don yin jigilar Maniyyata aikin Hajjin shekarar 2025 daga Nigeria zuwa kasar Saudiyya.

Hukumar ta fara aikin tantancewar tun daga ranar 27 ga watan Nuwamba zuwa 5 ga Disamba, tare da sanya matakai masu tsauri wajen tantance kamfanonin, a birnin tarayya Abuja.

Kamfanonin jiragen saman da aka tantance sun hadar da;

1. Max Air Limited.

3. Flynas.

4. Air Peace Limited.

5. Flyadeal.

6. Gyro Air Limited.

7.Trebet Aviation.

8. Umrah Air Limited.

9. Value Jet.

10.Umza Aviation Services Limited.

11.Aglow Aviation Support Services Limited.

12. Kiswah Logistics Services Limited.

13.Sokodeke.

14.CargoZeal Technologies.

Daga yanzu zuwa kowanne lokaci hukumar zata fitar da sanarwar kamfanonin da aka zaba don yin jigilar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here