Atiku ya taya John Mahama murnar lashe zaben shugaban kasar Ghana

0
68

Dan takarar shugaban kasar Nigeria na jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023 Atiku Abubakar, ya taya John Mahama murnar lashe zaben shugaban kasar Ghana, wanda aka gudanar a jiya Asabar sannan aka sanar da Sakamakon zaben a yau lahadi.

Atiku ya aike da sakon nasa zuwa ga Mahama tare da jam’iyyar sa ta NDC.

Hakan yazo bayan dan takarar shugaban kasar Ghana na jam’iyyar NPP mai mulki Mahamudu Bawamia ya amince da shan kaye tare da taya Mahama murnar lashe zaben a dazu.

Kawo yanzu dai hukumar zabe ta Ghana bata kammala sanar da Sakamakon a hukumance ba.

Jam’iyyar NPP mai mulkin kasar Ghana ta samu rashin nasara a mafi yawa daga cikin gundumomin kasar, musamman kujerun majalisar kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here