Ma’aikacin banki ya sace miliyan 18 na masu ajiya a bankin da yake aiki

0
55

Dubun wani ma’aikacin banki mai sacewa mutane kudi ta cika bayan bincike ya bayyana yadda aka gano makudan kudade a asusun bankin sa mabanbanta.

Mutumin ya kasance mai yin aiki a daya daga cikin rassan bankin Access dake Daura a jihar Katsina, da aikin sa shine kula da na’urar cirar kudi ta ATM.

Asirin ma’aikacin ya tonu bayan sace Naira miliyan 18 daga asusun masu ajiya.

Jaridar Aminiya, ta rawaito cewa, ana zargin jami’in, mai mukamin Mataimakin Mai Kula da ATM ne a bankin, ya sace kudaden ta hanyar hada baki da wani abokinsa wanda shi ma ma’aikacin bankin ne da ke garin Kafur.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu Naira miliyan 10 a asusunsa na bankuna daban-daban, da kuma tsabar kudi Naira dubu 366

Kakakin ’yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, sannan yace za’a kai shi kotu bayan gama bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here