Yunwa tayi ajalin kananun yara 800 a jihar Katsina

0
23

Wani binciken da Kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta MSF, ta gudanar ya bayyana cewa matsananciyar yunwa tayi yawa a jihohin arewa maso yamma a Nigeria.

Kungiyar tace a cikin shekarar 2024, da ake bankawa da ita, ta samu alkaluman cewa kananun yaran da suka mutu a sanadiyyar matsananciyar yunwa sun kai 800, a cikin asibitocin da Kungiyar ke yin aiki kadai a Katsina.

Hakan ya nuna cewa adadin ya zarce yawan haka in aka bi diddigin sauran asibitoci da gidajen al’umma, wanda za’a iya samun yaran da yunwa ta kashe ba tare da an kai su asibiti ba.

Babban abin takaicin shine ana zaton karuwar wadanda wannan matsala ka’iya shafa saboda tsadar rayuwa da ake cigaba da fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here