Takardar kudi ta Naira na cigaba da farfadowa akan Dalar Amurka

0
25
Farashin Dala zuwa naira
Farashin Dala zuwa naira

Takardar kudi ta Naira na cigaba da yin da yin sama a daidai lokacin da darajar Dala ke sauka kasa akan Naira.

Hakan ya faru sakamakon karancin masu siyan dalar da ake fuskanta musamman yadda masu kasuwancin canjin kudaden ketare ke neman wadanda zasu siya Dalar.

A yau juma’a an canjar da kowacce Dala daya akan naira 1,535, sabanin naira 1700, a kwanakin baya.

Yau shine kwana na uku a jere naira tana yin sama akan Dalar Amurka saboda tsarin da babban bankin Nigeria CBN, ya bijiro dashi na habbaka samar da kudaden ketare don magance matsalar karancin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here