Mataimakin gwamnan Borno ya tsallake rijiya da baya sakamakon lalacewar jirgin da suke ciki

0
33

Mataimakin gwamnan Borno, Umar Kadafur, tare da wasu fasinjojin jirgin Max Air, sun tsallake rijiya da baya sakamakon lalacewar jirgin da suke ciki.

Jaridar Vanguard, ta rawaito cewa Mataimakin gwamnan yana daga cikin mutane 100, da suke cikin jirgin na Max, lokacin da jirgin ya samu matsala sakamakon kamawa da wutar da injin jirgin yayi jim kaÉ—an bayan tashi daga filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Maiduguri a jiya Laraba.

Lamarin ya afku da misalin karfe 7 na daren laraba, yayin da jirgin ya dauki hanyar zuwa birnin tarayya Abuja.

Injin jirgin ya kama da wuta mintuna 10 da tashi, wanda bugar wani tsuntsu da yayi ta kawo masa matsalar.

Bayan haka, ne aka umarci Matukin jirgin ya gaggauta dawowa filin jirgin na Maiduguri don kiyaye afkuwar hatsarin da ka’iya janyo asarar rayuwar al’umma.

Da yake tabbatar da lamarin, wani ma’aikacin kamfanin Max Air ya ce, Jim kaÉ—an bayan tashin jirgin ya bugi tsuntsu a cikin iska, wanda ya sa É—aya daga cikin injunan sa ya kama wuta.

Sannan yace matukin jirgin ya yi aiki cikin gaggawa don tabbatar da lafiyar dukkan fasinjoji.

Kamfanin Max yayi gaggawar samarwa da fasinjojin wani jirgin don kaisu inda suka yi niyyar zuwa, yayin da wasu fasinjojin suka koma gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here