Yan kasuwar Kano sun yi alkunut saboda rashin wutar lantarki

0
38

Wasu daga cikin yan kasuwa kananu da matsakaita sun yi addu’o’in neman dauki akan yadda sana’o’in su ke neman lalacewa saboda rashin wutar lantarki tsawo kwanaki 70.

Yan kasuwar da suka yi sallah da alkunut da sauran addu’o’in sun kasance a yankin Dakata mai dauke da kanfanoni, da guraren kasuwanci, a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

:::Sanata Barau yakai kudirin samar da jami’a mai sunan Yusuf Mai Tama a Kano

Sun yi addu’ar ce don neman Allah ya kawo musu mafita da dauki dangane da halin da suka shiga.

Ana hasashen sama da mutum 10,000, lamarin ya shafa baya ga asarar miliyoyin kudade.

Tun lokacin da aka samu daukewar lantarki a arewacin Nigeria sakamakon lalacewar da tayi ake samun koma bayan wadatuwar wutar musamman a jihohin arewa, kuma hakan yana da babban tasiri wajen karya kananun yan kasuwar da ba zasu iya siyan man Gas din da zai basu wutar da suke bukata ba.

Wadanda abin yafi shafa sun hadar da masu kamfanoni, masu siyar da danyen kifi, danyen nama, Kankara, walda, da dai sauran sana’o’in dake bukatar wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here