Mutane sun fara dena tura naira dubu 10 kai tsaye saboda harajin naira 50

0
43

A ranar Litinin 2 ga watan Disamba 2024, ne bankunan Nigeria suka fara cirewa masu hulda dasu harajin naira 50 akan kowacce naira dubu 10 da suka turawa asusun ajiyar kudi.

Sabon harajin ya kasance abin kyama ga masu hulda da bankuna sai dai basu da wani zabi daya wuce yin hakuri, musamman a wannan lokaci da al’amuran kasuwanci suka koma hada hadar kudi ta bankuna.

Sabon harajin ya nuna cewa za’a dauki naira dubu daya idan aka turawa mutum naira dubu dari 2 zuwa asusun sa, sannan za’a dauki naira dubu 5, ga duk wanda aka turawa naira miliyan daya.

Saboda haka ne wasu suka yanke hukuncin cewa gara a tura musu naira 9999, sabanin naira 10,000, da manufar kaucewa sabon harajin.

Wasu kuma sunce bai kamata a biya wannan haraji ba, tunda gwamnati ta gaza samarwa da yan kasa aikin yi, to bai kamata su yan kasa su bata kudi ba.

A daidai lokacin da wasu ke cewa in har za’a yi amfani da harajin ta hanyar data dace hakan abu ne mai ma’ana.

Binciken masana harkokin tattalin arziki, ya ankarar da cewa ba kananun kudade za’a rika tatsa daga mutane ba, saboda yawan tura kudin da mutane keyi daga aausu zuwa wani asusun.

Sau da dama ana karbar haraji daga yan Nigeria, sai dai ana rasa wane amfani yake yiwa mutanen da suka bayar da shi.

Wannan abu zai kasance gaskiya idan aka yi duba ga fannin tafiya, tsaro, ilimi, ruwan sha, lantarki, hanyoyin sifuri, walwalar al’umma, aiki yi, da sauran su, wanda tabbas wadannan bangarori sune kadai za’a inganta talaka ya samu saukin rayuwa.

To sai dai hakan ya zama abin kaico, sakamakon cewa duk wadannan fannoni da aka lissafa za’a gane cewa a tabarbare suke tare da neman gagarumin gyara.

Da ana yin amfani da harajin da mutane suke bayarwa ta hanyar data dace tabbas wadannan bangarori zasu gyaru, tamkar irin na kasashen da yan Nigeria ke gani talbijin.

Bayan wannan haraji har yanzu akwai sauran rina a Kaba, yayin da gwamnatin tarayya ke kokarin tabbatar da sabuwar dokar haraji da wasu suka yi imanin cewa zata karya tattalin arzikin masu karamin karfi, da kuma kara tsadar kayan masarufi.

Tambayar a nan itace shin ya kamata talakan Nigeria ya rika biyan haraji ???

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here