Matafiya sun mutu bayan taka Bom a jihar Zamfara

0
82

Wasu matafiya sun rasu sannan wasu suka jikkata biyo bayan taka wata nakiya da ake kyautata zaton yan fashin daji ne suka dasa ta akan hanya don ta hallaka matafita.

Jaridar Punch, ta rawaito cewa akalla mutane 6, ne suka mutu yayin da 8, suka ji munanan raunika, lokacin motar tasu ta taka nakiyar a hanyar zuwa kauyen dan sadau, na karamar hukumar Maru dake Zamfara.

Motar data taka nakiyar ta kasance ta haya ce kirar Golf, wadda fashewar nakiyar ta yi raga-raga da ita yanda ba zata moru ba.

Kawo yanzu dai mahukunta basu sanar da komai dangane da harin ba, a daidai lokacin da aka gagara samun damar jin ta bakin gwanatin jihar Zamfara kan afkuwar lamarin.

Wannan shi ne karo na biyu da ake zargin ‘yan fashin suna dasa irin wannan nakiyar a mako guda, sakamakon a ranar Lahadin da ta gabata, maharan sun dasa wata nakiya a garin Maru da ke jihar ta Zamfara, da wata motar haya ta taka, kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin arewa maso yamma masu fama da kalubalen rashin tsaro musamman ayyukan yan fashin daji masu garkuwa da mutane da kuma kisa babu dalili.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here