Masu amfana da Boko Haram basa son a kawo karshen kungiyar—Zulum

0
40

Gwamnan jihar Borno, mai fama da rikicin Boko Haram Babagana Umara Zulum, yace akwai wasu boyayyun mutane dake amfanuwa da rikicin na kungiyar Boko Haram.

Gwamnan ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta BBC Hausa, inda yace an gaza cimma nasarar dakile kungiyar Boko Haram, da rikicin yankin tafkin Chadi saboda akwai masu amfana da rikicin wajen samun abin duniya.

:::Mutane sun fara dena tura naira dubu 10 kai tsaye saboda harajin naira 50

Zulum, yace mutanen ba zasu taba jin dadi ba in har aka wayi gari an kawo karshen rikicin na yankin tafkin Chadi.

Sai dai gwamnan na Borno bai bayyana sunan mutanen da yake zargin suna goyon bayan hakan ba.

Gwamnan ya ce duk da an samu ci gaba a yaƙi da matslar tsaron, amma a yanzu mayaƙan Boko Haram sun kwararo daga Chadi har sun kashe sojojin Najeriya da dama.

Ko a ƙarshen watan Nuwamba mayaƙan sun kai hari a wani sansanin sojin Najeriya na yankin ƙaramar hukumar Kukawa inda suka kashe sojoji uku yayin da kuma aka kashe mayaƙan sama da 10.

BBCHAUSA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here