Kotu ta kwace gidaje 753 a wajen tsohon jami’in gwamnati bisa zargin almundahana

0
66

Kotu ta kwace gidaje 753 a wajen wani tsohon jami’in gwamnati da ba’a bayyana sunan sa ba, bisa zargin almundahana, da wawure dukiyar al’umma.

Rukunin gidajen da aka kwace ya kasance a birnin tarayya Abuja.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ce ta shigar da karar wanda aka kwace gidajen daga wajen sa.

Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie, ne ya bayar da umarnin kwace gidajen a ranar Litinin.

:::Gobara ta kone shaguna masu yawa a Damaturu

Karbar gidajen da ke yankin Cadastral Zone C09, Lokogoma, a Abuja, shi ne kwacen kadarori mafi girma a lokaci guda da hukumar EFCC ta yi nasara yi tun da aka kafa ta shekara 21 da suka gabata.

Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Onwuegbuzie, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kasa kawo wa kotu dalilin da zai hana kwace kadarorin daga wajen sa, wadanda ake zargin ya mallake su ta haramtacciyar hanya, haka ne yasa aka tabbatar da cewa ya mallaki gidajen ta hanyar yin amfani da dukiyar al’umma, sannan a yanzu an bawa gwamnatin tarayya karadorin.

Sanarwar da EFCC ta fitar ta bayyana cewa, shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya bayyana hukuncin a matsayin karya gwuiwar masu sace dukiyar kasa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here