Ba dokar haraji ce tasa aka dauke daurin auren iyalan Barau daga Kano ba—Iyalan Ado Bayero

0
54

Iyalan tsohon Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero, sun ce ko kadan kudirin dokar haraji bashi da alaka da canja wajen daurin auren yar su Maryam Nasir Ado Bayero, wadda dan Sanata Barau Jibril, wato Jibril Barau, zai aura.

Shugaban kwamitin shirye shiryen daurin auren Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa daman bisa al’ada iyayen amarya sune suke zabar wajen daura auren yar su, inda yace an dauke daurin auren daga fadar Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, dake Nassarawa zuwa Abuja, saboda a saukakawa manyan mutanen da zasu halarci taron.

Yace manyan mutane daga cikin Nigeria da ketare ne suke son halartar taron daurin auren.

Idan za’a iya tunawa, tun bayan fitar sanarwar canja wajen daurin auren wasu daga cikin mutane ke alakanta hakan da kudirin dokar haraji, wadda ta dauki hankalin al’umma, musamman abinda wasu ke cewa Sanata Barau Jibril, na daga cikin masu goyon bayan samar da dokar.

Anyi imanin cewa dokar ka’iya kassara arewa da kuma daukaka darajar jihar Lagos.

Wasu sunce wadanda suka fusata akan kudirin dokar ka’iya kawo hargitsi ko tarnaki ga masu halartar taron daurin auren, sannan suka ce haka ne dalilin canja wajen daurin auren.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here