Yau ce ranar fara yin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a Nigeria.

0
77

Yau litinin 2 ga watan Disaba na shekarar 2024, itace ranar da aka tsara domin ma’aikatan lafiya su fara gabatar da allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a Nigeria, wadda kasar take sahun gaba a jerin kasashen da cutar tafi karfi.

:::Gwamnatin Kano Tana Sake Gina Hasumiyar data Rusa

Za’a fara yin allurar rigakafin ga kananun yara yan kasa da wata biyar da haihuwa.

Jihohin Bayelsa, da Kebbi, sune inda za’a fara aiwatar da rigakafin, sakamakon cewa bincike ya bayyana al’ummar jihohin a matsayin wadanda suka fi kamuwa da cutar.

Cutar zazzabin cizon sauro wadda aka fi sani da Malaria, na daya daga cikin cutukan dake addabar yan Nigeria, inda tafi kashe mata da kananun yara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here