A karon farko shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya kawo ziyara Afrika

0
64

A karon farko shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya kawo ziyara nahiyar Afrika, a matsayin sa na shugaban kasa, inda ya sauka a Cape Verde.

:::Farashin Dala

Daga nan zai wuce Angola inda ake sa ran zai bayyana yawan bashin da Amurka za ta bayar don taimakawa wajen gina sabon layin dogo mai tsawon kilomita 1,300, a kasar.

Layin dogon zai haÉ—a tashar ruwan Lobito ta Angola da yankin da ake sarrafa jan Æ™arfe na Zambia da kuma wuraren haÆ™ar ma’adinai na Cobalt dake Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Ana daukar aikin gina layin dogon a matsayin kalubale yayin da China ke neman mamaye fannin hakar a’adanai a nahiyar Afrika.

China ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ƙasashen Tanzania da Zambia a watan Satumba domin farfaɗo da layin dogo da ke yankin gabashin Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here