Za’a gurfanar da mai Maganin bindigar daya harbi kansa a gaban kotu

0
55

Wani mai maganin gargajiya, mai Ismail Usman, ya harba wa kansa harsashi a lokacin da yake gwajin maganin bindiga.

Daily trust, ta ruwaito cewa, lamarin ya faru a Kuchibiyi da ke Karamar Hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin yankin, mai suna Samson Ayuba, ya bayyana cewa a ranar alhamis data gabata ne lamarin ya faru yayin da mutumin ya ɗirka wa kansa harsashi Lokacin da yake yin ƙoƙarin gwada ingancin maganin bindigar da ya samar.

A cewar Samson, makwabtan mai Maganin bindigar ne suka yi gaggawar kai shi asibiti, ya faduwar sa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja Joesephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce sun samu kira kan cewa wani mai maganin gargajiya ya harbi kansa a daidai lokacin da yake gwajin maganin bindigar.

Adeh, tace bayan gwajin an tabbatar da cewa maganin ba zai bayar da kariya daga harbin bindiga ba.

Lokacin da jami’an tsaro suka gudanar da bincike sun gano wata bindigar gargajiya da layu waÉ—anda ya yi amfani da su wurin gwajin maganin bindigar.

‘Yan sandan sun kuma ce a halin yanzu suna ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba da kuma yunƙurin kashe kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here