Gwamnatin Kano ta dawo wa da jami’ar YUMSUK sunan ta na North West

0
123

Gwamnatin Kano ta dawo wa da jami’ar Yusuf Mai Tama Sule, (YUMSUK) sunan ta na asali wato North West.

Gwamnatin ta amince da sauya sunan lokacin zaman majalisar zartarwa ta jihar na ranar 21 ga watan Nuwamba 2024.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ne ya sauyawa jami’ar North West, suna a shekarar 2017 zuwa sunan Yusuf Mai Tama Sule.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kano Sunusi A. Kofar Na’isa, ya fitar yace gwamnatin Kano ta tsara samar da wata kwalejin ilimi mai sunan Yusuf Mai Tama Sule, a karamar hukumar Ghari, dan haka ne ta canjawa jami’ar suna a yanzu.

Haka zalika zaman majalisar zartarwar Kano ya amince da kara wa’adin lokacin gama aiki ga farfesoshi daga shekara 65 zuwa Shekaru 70, sai ma’aikatan makarantun gaba da sakandire da aka mayarwa lokacin ritaya zuwa Shekaru 65 daga shekara 60.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here