Bincike ya bayyana cewa ko inji daya baya aiki a matatar mai ta Fatakwal

0
176

Wani binciken da jaridar Punch, ta gudanar ya bayyana cewa babu ko da inji daya da yake yin aiki a matatar man fetur ta Fatakwal dake jihar Rivers.

Da farko shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ya sanar da cewa matatar ta fara tace man fetur a ranar talata data gabata, yana mai tabbatar da cewa bada jimawa ba za’a fara fitar da man zuwa ga yan kasuwa.

Sai dai bayan hakan wasu daga cikin al’ummar jihar Rivers, sun fito tare da bayyana cewa babu gaskiya ko kadan a maganar fara tace man fetur a matatar man Fatakwal, wanda mai magana da yawun kamfanin NNPCL ya fito tare da cewa masu zargin haka ba gaskiya suka fada ba.

Sai gashi a wata ziyarar gani da ido da wakilin jaridar Punch, ya kai a jiya juma’a, ya tabbatar da cewa babu wani aikin da ke gudana a matatar, a yayin da wasu ma’aikatan wajen suka bayyana masa cewa ana kan aikin gyara matatar wanda za’a iya kaiwa wani makon kafin kammalawa.

Tun a baya an sha saka lokacin fara aikin matatar amma hakan yana gagara, wanda sai da aka saka lokacin budewa ana fasawa har sau bakwai.

A ranar talata data wuce shugaban NNPCL, Mele Kyari, yace wai motocin dakon fetur dari biyu ne suke daukar mai a kowacce rana daga matatar ta Fatakwal.

Bayan sanarwar tasa an samu bayyana ra’ayoyi daga mutane masu cewa man da aka ce motoci suna dauka ba yanzu aka tace shi ba, inda aka ce mai ne dake cikin tankuna tsawon lokaci ba’a yi amfani da shi ba.

Daya daga cikin ma’aikatan matatar daya nemi a sakaya sunan sa ya ce babu wani aikin da suke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here