Farashin fetur ka’iya dawowa kasa da naira 1000—Dillalai

0
89
man fetur
man fetur

Yan kasuwar man fetur a Nigeria sun ce farashin man ka’iya yin kasa zuwa 900 ko 1000 daga yanzu zuwa lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.

Dillalan man fetur din sun ce hakan zai faru saboda yunkurin da matatar man fetur ta Dangote keyi a fannin mai.

Shugaban kungiyar masu gidajen mai ta kasa (PETROAN), Billy Gillis-Harry, da Kakakin kungiyar dillalan mai ta kasa (IPMAN), Chinedu Ukadike, ne suka bayyau Litinin data gabata.

A ranar lahadin data gabata ne matatar Dangote ta rage farashin litar daga 990, zuwa 970, ga yan kasuwa don saukakawa yan Nigeria, da kuma gode musu.

Hakan na zuwa bayan makonni da matatar Dangote ta sanya hannu da dillalan mai domin sayar musu da mai kai tsaye ba tare da saka bakin kamfanin NNPCL ba.

Gillis-Harry ya ce ragin farashin da matatar Dangote ta yi zai taimaki ‘yan Nijeriya wajen samun saukin man.

A cewarsa, da yiwuwar farashin zai ci gaba da sauka amma ya danganta da farashin danyen mai da kuma matatar Dangote.

Shima Ukadike ya sanar da cewa za’a samu farashin fetur mai sauki a lokaci bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here