Allah ya kare ni daga masu yi min fatan mutuwa—Obasanjo

0
58

Tsohon shugaban kasar Nigeria Olusegun Obasanjo, yace yana nan cikin koshin lafiya, duk da irin fatan da wasu yi masa na mutuwa.

Tsohon shugaban yace yana nan da ran sa da lafiya, amma wasu mutanen suke yi masa fatan mutuwa suna yada jita-jita, inda yace yana gani a kafafen sada zumunta wasu na yada jita-jitar cewa ya mutu, sannan yace Allah ya kare shi daga masu yin burin ganin hakan ta faru akan sa.

Ya sanar da hakan a lokacin da yake magana a garin Osogbo na jihar Osun, yayin buÉ—e titin Old-Garage/Oke-Fia da Gwamna Ademola Adeleke, na jihar Osun ya sake ginawa.

:::Za’a Gudanar da Sallar Rokon Ruwa a Kasar Saudi Arabia

  • Obasanjo yace na gaggauta sanar da ’ya’yana da dangina cewa labarin mutuwar ba gaskiya ba ne kuma ina nan da raina.

Obasanjo, ya yaba wa Gwamna Adeleke bisa nasarorin da ya samu a Osun, kuma ya shawarce shi da ya ci gaba da gudanar da ayyuka masu kyau.

A nasa jawabin, Gwamna Adeleke ya tabbatar wa mutanen Jihar Osun, cewa gwamnatinsa za ta kammala dukkanin ayyukan data faro ba tare da barin gibi ba.

Cikin ayyukan akwai gadoji biyu masu girma da suke gab da kammaluwa a Osogbo, kuma ana ci gaba da aiki a gadar Ile-Ife da kuma hanyar da aka ninka zuwa biyu a Ilesa, tare da aikin gina titi mai nisan kilomita 120, da aka kammala wanda gwamnan yace jihar bata aro kudi wajen gudanar da ayyukan da take yi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here