Gwamnatin Kano ta rufe kamfanonin Dantata da Mangal saboda haraji

0
61

Rashin biyan kudaden haarajin gwamnatin yasa gwamnatin Kano rufe kamfanonin Dantata & Sawoe.

Bayan wannan Hukumar tattara haraji ta Jihar Kano (KIRS) ta rufe babban ofishin kamfanin jiragen sama na Max Air da kuma kamfanin shinkafa na Northern Rice and Oil Mill, suma akan rashin biyan haraji.

Daraktan Kula da Basuka na Hukumar, Ibrahim Abdullahi ya ce an rufe guraren bayan samun umarnin kotu.

Ya ce an rufe kamfanin Ɗantata & Sawoe mallakin hamshaƙin attajirin Kano, Alhaji Aminu Ɗantata saboda bashin harajin albashi (PAYE) na shekara biyu (2021-2022) da ya kai Naira miliyan 241.

Kamfanin Max Air, mallakin Alhaji Sagiru Barau Manual babban attajirin Jihar Kastina, shi kuma an rufe shi saboda taurin bashin harajin shekara biyar daga 2017 zuwa 2022.

Jami’in ya ce an rufe kamfanonin ne bayan an yi ta rubuta musu takardu su biya kuɗaɗen amma suka ki biyan.

Ya ce dukkan kamfanonin za su ci gaba kasancewa a rufe har sai sun biya kuÉ—aÉ—en, yana mai cewa yin hakan ya zama dole.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here