Nigeria ta samu dala biliyan 20 saboda cire tallafin man fetur

0
76

Ministan kudi na Nigeria yace kasar ta ajiye kudaden da yawan su yakai dala biliyan 20 saboda cire tallafin man fetur, da kuma cire tallafin sauyin kudaden ketare.

Edun, ya sanar da hakan a bikin cikar Esther Waldo, kwanaki dari da zama shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, daya gudana a birnin tarayya Abuja.

Yace tallafin man fetur da tallafin canjin kudaden ketare sune ke cinye kaso 5 cikin dari na adadin kudaden da Nigeria ke samu a kowacce shekara, a lokacin da gwamnatin ke biyan su.

A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023, ne shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya sanar da cire tallafin man fetur, bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar, kuma haka ne yasa farashin man ke karuwa babu kakkautawa, tare da jefa al’ummar kasar cikin kunci da tsadar rayuwa.

Kawo yanzu dai talakawan Nigeria basu ga alfanun cire tallafin man ba, da mahukunta ke cewa cire tallafin yana da amfani.

Haka zalika, farashin canjin kudaden ketare yayi tashin gwauron zabi, a daidai lokacin da ake sauyar da Dalar Amurka kowacce daya akan 1750.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here