Bankin Access ya musanta zargin kwashewa masu ajiya naira miliyan 500

0
70

Bankin Access, dake huldar kasuwanci a Nigeria ya musanta zargin da akayi masa cewa ya kwashewa masu ajiyar kudi a cikin sa naira miliyan 500, daga asusun su.

Cikin wata sanarwa da bankin ya fitar jiya lahadi, a shafin sa na sada zumunta Access, yace ko kadan ba zai yiwu a samu aikata wannan rashin kwarewar aiki daga wajen su ba.

Tunda farko wani Vincent Otse, yayi zargin cewa bankin ya kwashewa masu ajiyar kudi a cikin sa kudaden da yawan su yakai naira miliyan dari 5, wanda yayi amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana zargin nasa ta cikin wani hoto mai motsi.

Bankin yace an janyo hankalin sa akan yaduwar faifan bidiyon da ake zargin su da kwashe kudaden, tare da bayyana cewa ba zasu zamanto masu yin wasa da dukiyar masu ajiyar kudi ba, tare da cewa suna bayar da tsaro ga duk asusun masu hulda dasu.

Daga karshe sun roki al’umma dasu yi whatsi da wancan zargin almundahana da akayi musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here