Rundunar Hisbah taje wajen masu yin Caca don yi musu wa’azi

0
57

Rundunar Hisbah ta jihar Kano, ta dauki aniyar samar da gyaran hali a tsakanin masu aikata laifukan badala da Caca a fadin Jihar.

Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr Mujahiddin Aminudden, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa babban kwamandan rundunar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya samar da wani atisaye mai suna gyara kayan ka, da manufar zuwa wajen masu aikata laifuka don yi musu wa’azi, su kiyaye aikata duk abubuwan da Allah ya haramta.

Dr. Aminudden, yace manufar samar da atisayen itace a dena yawan kama masu laifin don ganar dasu muhimmancin tuba saboda Allah ba saboda tsoron jami’an hukumar ba.

Haka ne yasa, rundunar ta shirya wani rangadi, na zuwa wajen da ake aikata laifukan shaye-shaye, Caca, lalata yara, shan giya da sauran su, tare da yi musu wa’azin su daina aikata laifin da suke yi, tare da cewa yawan kama masu laifin ba itace kadai hanyar gyara ba.

A wannan lokaci, an kai ziyarar zuwa guraren da ake aikata mabanbantan laifuka dake kan titin zuwa gidan Zoo, da titin zuwa gidan gwamnati, sai Flamingo, sai titin Murtala Muhammad way da sauran su, inda jami’an Hisbah suka bayyanawa mutanen da suka samu a wajen suna aikata ba daidai ba irin hukuncin da zasu tarar a wajen mahaliccin su.

Hisbah tace tana fatan hakan ya zama sanadiyyar gyaruwar masu aikata laifukan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here