Shugaba Tinubu yace yan Nigeria sun kusa fita daga kuncin yunwa

0
77

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na Nigeria, ya tabbatar da cewa yan kasar suna cikin kuncin rayuwa da yunwa, sannan yace nan bada jimawa ba za’a samu sauki saboda wasu tsare-tsare da yake bijirowa dasu na saukaka yanayin da ake ciki.

Tinubu, yace nan gaba yan Nigeria zasu fita daga halin kuncin rayuwa, yunwa, da sauran matsalolin da ake ciki.

Shugaban Ƙasar, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ƙulla yarjejeniyar inganta harkokin sarrafa naman dabbobi da wani kamfani a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil, a wani bigire na taron kasashen G20 masu karfin tattalin arziki, kamar yadda hadiminsa a fannin sadarwa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

Tinubu ya ce akwai wasu muhimman tsare-tsare da gwamnatinsa ta shimfiÉ—a domin kawo bunÆ™asa harkokin noma da kiwo a Nigeria don farfado da tattalin arzikin kasar da al’ummar ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here