Kungiyar ACF ta dakatar da shugabanta saboda ya kalubalanci Tinubu

0
67

Ƙungiyar Tuntuba ta Dattawan Arewa ACF ta dakatar da shugaban majalisar kolinta, Mamman Mike Osuman dangane da wasu kalaman da yayi a wani taron da Kungiyar ta yi ranar Laraba a Kaduna.

A wata sanarwa da ACF ta fitar ta musanta wasu bayanai da ke yawo inda ake cewa sun bayyana goyon bayan fito da dan takarar Shugaban Ƙasa daga yankin Arewa a 2027.

Cikin sanarwar da ACF ta fitar ta hannun Shugaba da Sakataren Cibiyar Amintattu, na kungiyar Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu da Alhaji Murtala Aliyu Wazirin Dutse, ta ce Osuman ya yi wannan kalamai ba da yawunta ba.

Sanarwar ta ce Osuman ya yi furucin ne ba tare da tuntuɓa ko neman shawarwarin sauran jiga-jigan ACF ba, saboda haka ra’ayinsa ne ya faɗa amma ba da yawunta ba.

Sai dai ƙungiyar ta kuma ce yankin na Arewa na fama da ƙangin talauci da matsalar tsaro da rashin ilimi, inda ta bayyana cewa matsalar yankin na hannun ‘yan Arewa.

A kalaman sa, Mike Osuman, ya bayyana cewa manufofin gwamnatiin Tinubu suna kawo wa talakawa koma bayan tattalin arzikin, musamman yan arewa, wanda yace akwai bukatar shugaban Nigeria Tinubu, ya sauya fasalin tafiyar da gwamnatin sa, don sanarwa talakawa sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here