Kaso biyu cikin uku na yan Nigeria basa samun lafiyayyen abinci—NBS

0
35

Hukumar kididdiga ta kasa NBS tace kaso biyu cikin uku na al’ummar gidajen Nigeria basa samun damar cin abinci lafiyayye, saboda tsananin rashin wadatar da yan kasar ke ciki.

NBS tace ta gano hakan bayan wani binciken data gudanar, inda tace abincin da yan Nigeria suke ci baya dauke da ingantattun sinadarai masu kara lafiya.

Binciken da hukumar ta gudanar ya mayar da hankali ne kan karuwar talauci a tsakanin gidajen Nigeria da irin tasirin da hakan ke yi wajen raguwar sayen abubuwan bukata sakamakon tashin farashinsu.

Haka kuma binciken ya gano cewa kashi 63.8 cikin 100 na gidajen na cin abinci mara yawa saboda rashin kudi.

Rahoton binciken yazo kasa da wata daya bayan da wani rahoto da gwamnatin Najeriya ta fitar tare da tallafin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa ‘yan Æ™asar fiye da miliyan 33 za su fuskanci matsalar Æ™arancin abinci a 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here