Ahmad Musa, ya yafewa masu haya a shagunan sa kudin hayar shekara guda

1
74

Fitaccen dan kwallon kafar Nigeria Ahmad Musa, ya yafewa masu haya a shagunan sa kudin haya na shekara guda saboda yanayin tabarbarewar tattalin arziki.

Ahmad Musa, ya yafe kudin hayar ne ga mutanen dake yin kasuwanci a shagunan sa dake MYCA-7 Plaza, dake kan titin zuwa gidan Zoo, a jihar Kano.

Ya sanar da wannan aikin alkairi a lokacin da yakai ziyarar gaisuwa ga mazauna shagunan da kuma jajantawa juna irin halin kuncin rayuwa da ake ciki, wanda yayi hakan don saukaka musu wajen tafiyar da kasuwancin su a wannan lokaci.

Babban wajen kasuwanci na MYCA-7 Plaza, dake Zoo Road, na daya daga cikin guraren da ake yin sana’o’in dogaro da kai, da taimakawa tattalin arzikin al’umma.

Daga karshe wannan aikin alkairi da Ahmad Musa, yayi ya zama zakaran gwajin dafi musamman ga masu wadata, kuma hakan zai taimaka in wasu suka kwaikwayi halin tausayin masu karamin karfi.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here