Rikicin sojoji da yan sanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum daya

0
74

Wani rikicin daya faru tsakanin soja da yan sanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum daya, da yazo wucewa ta wajen da abun ke faruwa.

Rikicin wanda aka yi a ranar Laraba, ya faru ne a yankin Ugwuachara, a jihar Ebonyi, bayan an samu sabani tsakanin Æ´ansanda masu bincikar motoci a hanya da wani soja wanda yazo wucewa a kan babur.

Wani da lamarin ya faru a gaban idon sa ya ce jami’in sojan ne ya Æ™i amince a binciki babur É—insa, wanda hakan tasa dan sandan dake binciken ababen hawan yayi yunkurin kama babur din sojan, daga wannan ne aka yi harbin da ya hallaka wani mai wucewa wanda bai ji ba bai gani ba, sannan mutane uku suka ji rauni.

Kwamishinar Æ´ansandan jihar Ebonyi, Anthonia Uche-Anya ta tabbatar da aukuwar lamarin a tattaunawarsa da tashar Channles ta wayar tarho.

Ta ce da sojan da É—ansandan duk suna hannu, kuma ana cigaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here