Kotun duniya ta bayar da umarnin kama Fira-Mininstan Isra’ila saboda kisan Falasdinawa

0
58

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaron kasar Yoav Gallant da kuma wani jami’in Hamas, kan aikata laifukan yaki a Gaza.

Karanta karin wasu labaran:::Majalisar dattawa ta amince da bukatar Tinubu ta nada mashawarta na musamman guda 20

Hakan ya biyo bayan kiraye-kirayen da wasu kasashen duniya keyi na ganin an hukunta Netanyahu, akan abinda suka kisa take hakkin bil-adama, da sojojin Isra’ila ke yiwa Falasdinawa, musamman mata da kananun yara.

Kasashen Afrika ta kudu da Turkiyya da gaba-gaba wajen ganin an hukunta Netanyahu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here