Damar siyan gawayin girki na neman gagarar talakan Nigeria

0
74

Lamarin tsadar rayuwa, da tabarbarewar tattalin arzikin yan Nigeria kullum karuwa take, a daidai lokacin da mafi yawancin masu karamin karfi ke neman rasa damar mallakar makamashin da zasu yi amfani da shi wajen yin girki girken abinci don yin rayuwar yau da gobe.

Tsadar makamashi ta kunshi kowanne irin makamashi mutum yake amfani da shi, daga kan Gas, kalanzir, gawayi, da itace.

Mawadata sun fi amfani da makamashi na Gas saboda yana da saukin ma’amala da rashin lalata wajen aiki, yayin da marasa hali suka fi amfani da gawayi ko itace wajen yin girki.

Tunda aka cire tallafin man fetur ake samun hauhawar farashin kayyakin masarufi ta kowanne bangare ba tare da kakkautawa ba.

A halin yanzu tsadar gawayi tafi damun talakawa a yayin da kwanon gawayi daya ya kai farashin naira 400, fiye da farashin da ake siyar da kwanon shinkafa a shekarun baya.

Kafin yanzu ana siyar da kwanon gawayi akan naira 150, 200, zuwa 250, sai buhun sa da ake siyarwa akan naira 6000, amma yanzu farashin buhun yakai naira dubu 11.

Bayan tsadar da gawayi yayi ana shan wahala kafin samun sa a wajen masu siyarwa, a daidai lokacin da farashin Gas kilo 12 yakai naira 18000.

Hakan ya haifar da karin kunci ga talakawa, sakamakon rashin wadatar da ake ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here