An fara yada jita jitar mutuwar Bello Turji

0
100

Wasu daga cikin al’umma sun fara yada labarin mutuwar fitaccen dan ta’adda daya addabi jihohin Zamfara da Sokoto, wato Bello Turji.

Masu yada Wannan labari sun ce jami’an tsaron Nigeria ne suka hallaka Turji, bayan harin kwantan bauna da suka kai masa ranar talata a maboyar sa dake jihar Sokoto.

Sai dai Kawo yanzu babu wani tabbas akan mutuwar Turji, daga bangaren rundunar sojin Nigeria ko kuma daya daga cikin fannin tsaro.

Masu yada jita jitar mutuwar Bello Turji, sun ce mazauna yankunan da Turji, ya addaba sun fara nuna farin cikin su da fitowar labarin rasuwar tasa.

Abin jira a gani shine fitowar sanarwar kisan nasa daga jami’an tsaro, ko kuma bayyanar gawar sa, saboda har yanzu babu wata hujja akan kisan.

Bello Turji, dai fitaccen dan ta’adda ne da yayi suna wajen yin garkuwa da mutane, kisan mutane babu dalili, sace dabbobi da Sauran ayyukan ta’addanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here