Yan ta’adda sun kone gonaki, da sace mutane a jihar Zamfara

0
53

Wasu yan ta’adda sun kone gonakin manoma da dama wuta tare da yin garkuwa da mutane masu yawan gaske a wasu daga cikin kauyukan Jihar Zamfara.

Da fari yan ta’addan sun fara kai hari garin Farin Ruwa da ke karamar hukumar Maru tare kone gonakin manoma.

A kauyukan Wanke da kuma Zargada, ma an fuskanci wannan iftila’i na kone amfanin gona daga yan bindiga

Mazauna yankunan da ke iyaka da jihar Kebbi, a Zamfara sun ce yan bindigar sun janyowa mamoman babbar asara ta masara, Wake da Auduga, har ma da sauran amfanin gona.

Mazauna yankin sun shaidawa BBC cewa, maharan sun kawo hari gungu gungu tare da cinna wa gonakin masara da wake da dawa wuta, abin da kuma ya haifar da asara mai yawa.

Bayan wannan danyen aiki da yan bindigar suka yi sun kuma yi garkuwa da wasu mutane .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here