Wike ya amince a biya mafi karancin albashi na 70,000 ga ma’aikatan Abuja

0
66
Nyesom-Wike
Nyesom-Wike

Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya amince da naira dubu 70 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnati dake Abuja 

Mai rikon mukamin shugaban ma’aikatan Abuja Grace Adayilo, ce ta sanar da hakan a ranar litinin.

Karanta karin wasu labaran:PDP zata hukunta mininstan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike

Sanarwar tace Wike, ya bayar da umarnin biyan biyan mafi karancin albashin don inganta ayyukan ma’aikatan dake karkashin kulawar sa.

Shugabar ma’aikatan ta Abuja, tace Wike, ya Kuma bayar da umarnin biyan ariyas ga ma’aikatan na tsawon watanni 3, wanda za’a fara daga watan Nuwamba na shekarar 2024, don inganta walwalar ma’aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here