Shugaban Nigeria ya gabatar da jawabi a taron G20

0
81

Shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da jawabi a taron kungiyar kasashen duniya 20, masu karfin tattalin arziki wato G20, dake gudana a birnin Rio de Janeiro, na kasar Brazil.

Shugaban Ƙasar Brazil, Lula da Silva, ne ke karbar bakuncin taron a matsayin sa na shugaban kungiyar G20, da wa’adin sa zai kare a karshen watan Nuwamba.

Taron ya mayar da hankali akan tattauna batutuwan tabbatar da muradun Karni, tattalin arziki, da kuma inganta muhalli, hadi da yin garambawul a fannin tafiyar da al’amuran gwamnati.

A lokacin jawabin sa, Tinubu, yayi alkawarin magance kalubalen yunwa da talauci a Nigeria, da habbaka cin gaban muradun Karni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here