An kori ma’aikatan EFCC daga aiki saboda aikata lefin cin hanci

0
54
Ola Olukoyede

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC Ola Olukoyede, ya sanar da cewa an kori ma’aikatan hukumar su biyu saboda zargin da akeyi musu na aikata laifin cin hanci da rashawa.

Ola, ya bayyana hakan a Abuja lokacin bude taron shekara-shekara akan bibiyar aikata laifuka karo na 6, wanda gidauniyar cigaban dokoki ta shirya.

Karanta karin wasu labaran:Kotu ta hana EFCC kama Yahaya Bello

Kamfanin dillacin labarai na Nigeria NAN, ya rawaito cewa za’a kwashe kwanaki 5, ana aiwatar da taron, da za’a tattauna yanda za’a magance matsalolin tattalin arziki da tsaro a kasar.

Yace an kori ma’aikatan ne makonni biyu da suka gabata, sannan za’a gurfanar dasu a gaban shari’a don hukunta su, inda shugaban hukumar yace ba zai yiwuwa a samu hannun jami’in hukumar a laifin aikata cin hanci ba tare da daukar mataki akan sa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here