Dangote zai rika baya yan kasuwa man fetur lita miliyan 240 kowanne wata

0
69

Matatar man fetur ta Dangote, ta yi tayin bawa dillalan man fetur, mai lita miliyan 60 a kowanne mako, wanda ya tasamma lita miliyan 240, a kowanne wata.

Bayyana hakan da matatar tayi yazo a daidai lokacin da, Dangote ke kokarin tattara dalolin da zai siyo danyen man fetur daga kasashen waje don habbaka yawan man da yake tacewa.

A ranar lahadi data gabata dillalan man sun ce an fara samun raguwar farashin fetur sakamakon gasar dake tsakanin masu Sana’ar siyar da man masu shigo da shi daga ketare, wanda kamfanin NNPCL da sauran yan kasuwa suka siyo lita biliyan 2, na tataccen man cikin kwanaki 42.

Lokacin da yake zantawa da jaridar Punch, sakataren kungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike, yace dillalan man zasu dauki duk adadin man da suke so daga matatar Dangote, inda ya sanar da cewa dillalan man fetur a Nigeria sune suka fi yin jigilar mafi yawancin man da ake shigowa dashi kasar.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta bawa yan kasuwa damar siyan man fetur kai tsaye daga matatar Dangote ba tare da kamfanin NNPCL ya shiga tsakanin su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here