Manoman birnin Gwari sun yi asarar fiye da miliyan 100 saboda harin yan ta’adda

0
59

Hare haren yan ta’adda ya janyowa mamoman karamar hukumar Birnin Gwari, ta jihar Kaduna asarar kudaden da yawan su yakai naira miliyan 100, a wannan shekara.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Gwari, Bashir Zubairu, yace an tafka asarar a gonakin masarar da manoman suka shuka.

Bashir, ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai, akan wani harin da yan bindiga suka kaiwa al’ummar Birnin Gwari, a makon daya gabata.

Ya ce idan har gwamnati ta gaza magance irin wannan babbar masifa to jama’a ba su da wani zabi daya wuce su kare kansu da kansu ta hanyar daukar makamai.

Yace yan bindigar suna yin wannan danyen aiki a matsayin daukar fansar kwace musu makamai da akayi inda suka dauki aniyar cigaba da kaiwa al’ummar Birnin Gwari hari.

Rahotanni sun bayyana cewa harin da aka kai a gonar masara a ranar Lahadin da ta gabata ya faru ne kasa da sa’o’i 48 bayan shugabannin addini da na al’umma sun gana da shugabannin ‘yan bindiga a yankin, inda suka tattauna batun zaman lafiya da su.

Dangane da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma, dan majalisar ya ce mutanen kauyukan da abin ya shafa da suka yi asarar dukiyoyinsu da ‘yan uwa a sakamakon hare-haren ya kamata a biya su diyyar asarar da suka yi.

Ya kara da cewa ba zai yiwu a zauna da ’yan bindiga a cikin yarjejeniyar zaman lafiya ba, daga baya a ba su makudan kudade, baya ga dukiyar da suka kwace daga hannun mutanen kauyukan da ba su ji ba ba su gani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here