Yan Nigeria miliyan 14 sun sake shiga cikin talauci—–Bankin Duniya

0
207
World Bank on glass building. Mirrored sky and city modern facade. Global capital, business, finance, economy, banking and money concept 3D rendering animation.

Wani rahoto ya bayyana cewa Karin yan Nigeria miliyan 14 sun sake afkawa cikin kangin talauci da kuncin rayuwa a wannan shekara ta 2024.

Bayanin hakan ya fito cikin wani rahoton Bankin Duniya da yayi bayani kan yanayin talaucin da ke faruwa a kasashen duniya.

A cewar rahoton, kaso 47 na ‘yan Nijeriya a halin yanzu suna rayuwa cikin rukunin talakawan duniya na yin rayuwa a kasa da dala 2.15 a rana.

Bankin duniya ya ce, ana harsashen talaucin ka iya zuwa kaso 52 cikin dari nan da shekarar 2026, don haka akwai bukatar gwamnatin Nijeriya ta tashi tsaye wajen bijiro da shirye-shiryen da za su kawo sauki da cero jama’a daga cikin wannan yanayin na talauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here