ICPC zata tuhumi ma’aikatan INEC kan zargin almundahana a zaben gwamnan Edo

0
61

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka makamantan su (ICPC), ta ce za ta binciki wasu korafe korafe da aka gabatar kan jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) dangane da zaben gwamna da aka gudanar a Jihar Edo kwanakin baya.

Idan za a iya tunawa, hukumar zabe ta bayyana Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 21 ga watan Satumba, 2014 a Jihar Edo.

Mai magana da yawun hukumar ICPC, Demola Bakare, ya tabbatar da cewa an samu wasu korafi a kan wasu jami’an hukumar zabe kan almundahanar kudade.

Wasu rahotanni sun bayyana yadda masu sa ido kan zaben jihar a makon da ya gabata suka mamaye hedikwatar hukumar ICPC inda suka shigar da kara kan INEC.

Masu sa idon wadanda akasarinsu lauyoyi ne karkashin inuwar ‘Tap Initiatibe’, sun bukaci da a kama jami’an hukumar tare da gurfanar da su a gaban kuliya bisa zargin buga takardar sakamako zabe guda biyu (EC8A).

Sai dai mai magana da yawun hukumar ta ICPC ya shaida cewa, a duk lokacin da suke yin wani bincike ba za su bayyana shi a fili ba har sai an kammala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here