Fashewar motar Gas ta jikkata mutane a jihar Katsina

0
59

Mutane da dama ne suka jikkata sakamakon fashewar gas data auku a Magama Jibiya akan iyakar jihar Katsina, wanda hakan yayi sanadiyyar lalacewar ababen hawa masu yawa da gidaje.

Fashewar ta afku a yau juma’a.Fashewar ta faru a wani gidan mai, mai suna Walidan, wanda aka danganta lamarin da fataucin gas daga Jamhuriyar Nijar zuwa Nigeria.

Shehu Umar, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa wata motar dakon mazubin gas da aka ajiye tsawon kwanaki a gidan man na iya haddasa fashewar sakamakon wani tartsatsi daga wayar motar dakon gas din.

Wasu mutanen da abin ya faru a kan idon su sun tabbatar da cewa mutane da dama sun sami raunuka, yayin da gidaje, da motoci, da makarantu a kusa da wurin suka lalace saboda tartsatsin wuta.

Mazauna yankin sun nuna damuwa kan fataucin gas ba tare da izini ba, suna zargin cewa rashin kulawar hukumomi ne ya haifar da wannan musifa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here