Sojojin Nigeria sun lalata matatun man fetur 59

0
68

Shalkwatar tsaron Nigeria tace sojoji sun lalata haramtattun matatun man fetur 59, a kudancin kasar, tare da kama barayin fetur 40.

Rundunar tace an kuma kama lita kusan dubu daya na danyen man da tataccen man lita 4,980, sai man Diesel lita 175,075.

Daga bangaren arewa kuwa shalkwatar tace jami’an ta sun hallaka yan ta’adda masu yawa musamman mayakan ISWAP, a yankin arewa maso gabas.

Daraktan yada labarai na shalkwatar Manjo Janar Edward Buba, ne ya sanar da hakan a ranar alhamis.

Yace kashe yan ta’addan da suka yi ya sanya a yanzu bata garin so suke su dauki sabbin mayakan, amma yace jami’an tsaro sun gano hakan da kuma kokarin daukar matakan dakile manufar daukar sabbin mayakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here