Matar tsohon gwamnan Ondo ta kwatanta Nigeria da gandun namun daji

0
77

Uwar gidan tsohon gwamnan jihar Ondo Marigayi Rotimi Akeredolu, Betty Akeredolu, ta bayyana kasar Nigeria a matsayin kasar da bata da maraba da gandun namun daji wato Zoo a turance.

Betty, ta bayyana hakan a shafin ta na X.

Ta yi Wannan kalami a lokacin da take yin tsokaci dangane da yanayin gudanar da zaben shugaban kasa a Nigeria da kuma zaben shugaban kasar Amurka daya gabata a kwanakin baya.

Tace a shekarar 2023, an shafe kwanaki 5, ana lissafin kuri’ar zaben mutane miliyan 25, na shugaban kasa a Nigeria, amma a Amurka kuri’u miliyan 155, aka kada sannan aka lissafa su ciki awanni 10, kuma haka ne yasa ta ke ganin ba’a yin abunda ya dace a Nigeria.

Sai dai masu amfani da shafin na X sun caccaki Betty, wadda ta rika kokarin kare kanta, hakan bai yiwu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here