Hukumar kiyaye hadura ta shirya rage afkuwar hadura na karshen shekara

0
72

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC reshen jahar Kano, ta fito da sabbin dabarun takaita afkuwar haduran ababen hawa da ake yawan samu musamman a lokacin da ake yawan tafiye tafiye saboda karewar shekara.

Kwamandan hukumar na Kano, Umar Matazu, ne ya sanar da hakan, lokacin bikin sauyawa jami’an hukumar 61, yanayin aikin su, duk dai a karkashin FRSC.

Ya kuma kaddamar da wasu sabbin motocin sintiri na rundunar guda biyu wanda yace tabbas zasu taimakawa jami’an su a kokarin da suke yi na takaita yawaitar hatsari akan tituna da fadin Jihar Kano.

Kusan kowacce shekara in tazo karewa akan samu yawaitar hatsari akan tituna, wanda hakan baya rasa nasaba da yawan tafiye tafiye zuwa garuruwa don gudanar da bukukuwan sabuwar shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here