Yan ta’adda sun kone gonaki kafin girbe su a jihar Kaduna

0
81

Wasu yan ta’adda sun kone gonakin masara shida kafin a girbe su a kauyukan Kwaga da Unguwar Zako da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Wannan mummunan aiki ya tayar da hankalin al’ummar kauyukan, musamman masu gonakin da abin ya shafa.

Daya daga cikin masu gonakin, Malam Kabiru Halilu Kwaga, ya shaida cewa a shekarar data gabata ya noma buhu 160 na masara a gonar, kuma a bana yana kyautata zaton samun fiye da haka, amma suka kona gonar kafin ya amfani ko da buhu daya.

Wani mai suna Malam Surajo Kwaga, ya ce buhu 40 ya samu a gonar sa bara, amma bana an kone ta bai samu komai ba.Shi kuma Malam Dan Gido, da ya samu buhu 50 a bara, ya ce ya yi fatan samun kimanin buhu 65 a bana.Malam Jibril Kwaga da ya rasa amfanin gonarsa a wannan mummunan hari ya yi fatan Allah Ya mayar musu da mafi alheri.

Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban Kungiyar Masu Kishin Yankunan Birnin Gwari, Ishaq Usman Kasai, ya yi zargin cewa ’yan fashin dajin da suka kona gonakin, yaran wani dan ta’adda Yellow Jamburos ne, da ke addabar yankin.

An yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, amma hakan bai samu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here