Gwamnatin Kano tace Ganduje ya bar mata bashin naira miliyan dubu 63

0
35
Gwamna Ganduje
Gwamna Ganduje

Gwamnatin jihar Kano tace tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, ya bar mata gadon bashin naira biliyan 63 da miliyan miliyan 508 da dudu 24 da dari 580.

Ofishin dake kula da basussuka na jihar ne ya sanar da hakan inda yace bashin ya kunshi na cikin gida da kasashen ketare.

Karanta karin wasu labaran:::An rantsar da sabon gwamnan jihar Edo a yau litinin

Shugaban ofishin Dr. Hamisu Sadi Ali, ne ya bayyana hakan, lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi akan basukan da ake bin Gwamnatin Kano.

Yace Abba Kabir Yusuf, wato gwamnan Kano na yanzu ya gaji bashi mai yawa daga Ganduje, amma yana rage yawan basukan a hankali, tare da cewa har yanzu gwamnatin Abba bata taba cin bashin ko kwandala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here